28 Disamba 2017 - 16:24
Turkiyya : Musulmin Duniya Ba Zasu yi  Sakaci Kan Birnin Qudus Ba

Shugaban kasar Turkiyya ya bayyana cewa; Birnin Qudus mallakin al'ummar musulmi ne, kuma ba zasu taba yin sakaci kan ci gaba da kare birnin ba

A taron manema labarai da ya gudanar da takwararsa na Tunusiya a ziyarar aikin da ya kai zuwa kasar Tunusiya : Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdugan ya bayyana cewa: Al'ummar musulmi a duk yadda suke a duniya suna daukan birnin Qudus a matsayin fadar mulkin Palasdinu ne kamar yadda yake a dokokin kasa da kasa, don haka matakin gwamnatin Amurka ta maida ofishin jakadancinta zuwa birnin na Qudus lamari ne da ya yi hannun riga da doka.

Har ila yau shugaban kasar ta Turkiyya ya yi suka kan matsayin kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya yana mai cewa: Duniya zata amince a kan matsaya daya amma a ce wasu tsirarun kasashe biyar kacal zasu iya rusa wannan matsaya da sunan hawa kan kujerar naki.